Ko ka san Amfanin Masara Bai Tsaya Ga TUWO Ba Kawai?

Must Try

MASARA NADA DUMBIN AMFANI GA LAFIYAR DAN ADAM, IN JI MASANA ….

KAN MASARA

Asami kan Masara wato Furen da takeyi a saman ta, asa Bagaruwa guda a dafa ana sha sau 2 Kwana 7, za’a sami lafiya daga kowanne irin Tari

GEMUN MASARA

A dafa shi asha kamar shayi Safe da Yamma
yana maganin ciwon koda.

Yana sauke Hawan Jini

Yana Magani Matsalolin Mafitsara (Bladder)

Yana Maganin Ciwon Gabobi

Yana karfafa Garkuwar Jiki

Yana Rage Teba

Yana Daidaita Suga

Yana Maganin Tsakuwar koda

Yana Maganin Rikicewar Al’adar Mata.

TOTUWAR MASARA

Ana daka busashshiyar Totuwar Masara a kwaba Tokar da man Shanu, tana maganin kowacce irin cutar fata Idan ana shafawa

Ana dafa Tsaftatacciyar Busashshiyar Totuwar Masara asaka Zuma asha kamar shayi tana maganin Kuturta.

GANYEN MASARA

Ana hada ganyen Masara dana Darbejiya a dafa asha karamin kofi sau 2 a rana yana sauke Kumburi.

MASARA GASASHSHIYA

Cin Gasashiyar Masara na ragewa mutum Kitse mara amfani a jikin shi
tana kawar da cututtukan uwar hanji

MASARA DAFAFFIYA

Tana kara Lafiayar Ido da kara Inganta lafiyar kasusuwan kjikin dan Adam

TUWON MASARA
Tuwon Masara nada matukar amfani amfani ga jikin dan Adam
musamman Tuwon Datsa

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img