pornhub

Magidanta Sun Koka Kan Tsadar Shinkafa Ýar Gida A Kano

Must Try

Magidanta da ƴan kasuwa a jihar Kano sun nuna damuwa kan karuwar kudin Shinkafa yar’gida yayin da farashin ta ya ke cigaba da hauhawa.

Binciken kasuwanni da aka gudanar ya nuna cewa buhun Shinkafa yar’gida mai nauyin kilogram 50 ana siyanshi akan dubu 47,000 farashin da shi ne mafi tsada da aka taba samu wanda ya sabawa farashin dubu 30,000-35,000 da aka siyar da buhun shinkafar a karshen shekarar da ta gabata.

A cewar wani magidanci mazaunin Unguwar Kawo a karamar hukumar Nassarawa ta jihar Kano, Malam Musa Hamisu, Shinkafa ita ce abincin da kusan kowane iyali ke amfani da ita, amma yanzu ta zama mafi tsada a dalilin haka ba da dadewa ba za ta gagari mutane da dama.

Ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa ko a cibiyoyin sarrafa Shinkafa yar’gida kamar Bunkure da Kura da Gezawa ana siyar da buhun Shinkafa mai nauyin 100 kilogram sama da dubu 80,000.

Abinda ya fi ban tsoro shi ne farashin yana ci gaba da tashi kowace rana. Damuwar ita ce lokacin azumi yana gabatowa kuma daga dukkan alamu, farashin shinkafa zai ci gaba da hauhawa mai yiwuwa ya kai dubu 60,000 a lokacin azumi.

Wani mai sana’ar shinkafa, Alhaji Maikano Bello,ya bayyana cewa kowane ton na shinkafa sanfarera ana siyar da shi akan dubu 45,000 ba kamar dubu 32,000 da aka siyar a watan da ya gabata ba.Tsananin bukatar shinkafa daga manya da kananan cibiyoyin sarrafa shinkafar da kuma bukatar shinkafa yar’ Najeriya daga makwabtan kasashe ne yake da alhakin tsadar shinkafa da ake fuskanta kwanan nan.

Yanzu mutane sun gwammace su rika cinikin shinkafa a kasashen da ke makwabtaka da mu, saboda nairar Najeriya ba ta da daraja fiye da kudin su.Suna siyan kaya da sauki ta hanyar ciniki da naira, su rika siyarwa da kasashen waje ta haka suke amfani da y’an Najeriya wajen samun riba.

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img