Farashin Shinkafa zai iya faɗuwa kwanan nan a Najeriya

Must Try

Akwai yiwuwar farashin tsabar shinkafar da ya yi yashin gwauron zabo a ’yan kwanakin nan ya fadi warwas sakamakon saukar farashin samfarerarta a sassan Najeriya, kamar yadda binciken jaridar Daily Trust ya gano.

Bayanai sun nuna tan din samfarerar shinkafar da a kwanakin baya ya kai Naira 420,000, yanzu ya sauko zuwa 360,000.

Binciken namu ya gano cewa faduwar farashin ba zai rasa nasaba da zuwan sabuwar shinkafar da aka noma da daminar bana ba, kuma ake aikin girbinta a sassan Najeriya daban-daban.

Idan za a iya tunawa, a cikin wata ɗaya, farashin buhun tsabar shinkafa mai nauyin kilogiram 50 ya tashi daga kimanin Naira 36,000, zuwa kusan 48,000.

’Yan kasuwa dai na alaƙanta tashin farashin shinkafar a wancan lokacin saboda wahalar da samfarerar ta yi a kasuwa, da kuma karuwar kudin da ake kashewa wajen sarrafa ta, saboda tsadar kayayyaki irin su man dizal.

A cewar wani mai sana’ar gyara shinkafar a Kano, faruwar hakan ta sa an sami raguwar farashin samfarerar shinkafar, kuma ana sa ran ita ma tsabar za ta sauko nan ba da jimawa ba.

“Zan iya tabbatar maka da cewa nan ba da jimawa ba, farashin shinkafa zai fadi warwas saboda tan din ta da a baya ake sayarwa N420,000, yanzu ya dawo N360,000. Muna kuma sa ran yayin da ake ci gaba da girbin shinkafar damina, farashin zai ci gaba da sauka,” kamar yadda majiyar da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana mana.

To sai dai daya daga cikin manoman shinkafa a Kano na cewa duk da akwai fargabar samun fari a wasu sassan Jihar, amma akwai alamun cewa damunar bana tana kyau.

A farkon watan nan ne dai ƙungiyar Abinci da Noma ta Duniya (FAO) ta ce farashin shinkafa a duniya ya kai matsayin da bai taɓa kaiwa ba cikin shekara 15 a watan Agusta.

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img