Amfani da Takin Gargajiya na ƙara inganta ƙasar Noma- Auwal Idris

Must Try

Aminu Halilu Tudun Wada

Yin amfanin da Takin Gargajiya da aka sarrafa shi a zamanan ce na bunƙasa ƙasar Noma tare da inganta ta , ta da amfanin Gona da aka Noma.

Masani kana ƙwararre akan sarrafa kayan feshin maganin ƙwari da Takin,na gargajiya , Malam Auwal Idris ne ya tabbatar da hakan a zantawar sa da Jaridar Al’amuran da suka shafi harkokin Noma ta FARMERS VOICE NG, da ake wallafawa ta Internet.

Malam Auwal , ya ce feshin maganin ƙwari mara sinadarin Chemicals, wanda aka sarrafa na ƙara inganta lafiyar al’umma da kayan amfanin Gona, da hakan ba zai taba zama barazana gare masu amfani da nau’ikan Abinci kala -kala ko Adana su na tsawon lokaci ba.

” A lokacin da mutane suka maida hankali wajen neman Taki na Zamani mai dauke da sinadarai na Chemicals ina mai basu shawara da su karɓi fasahar zamani da ke kara shigowa a yanzu haka ta hanyar sarrafa Taki da magunguna na feshi ga shuka wanda basu da sinadaran Chemicals”.

” Akwai alafanu mai yawa ga Manoma da Miliyoyin mutane in har aka canja tsarin amfani da kayan dake dauke da chemicals musamman ta bada kariya daga kamuwa da cututtuka da suka haɗa dana Daji (Cancer ), Kuraje, Kumburin Ciki da makamantansu, sannan ita kanta ƙasa da ake Noma ba zata samu matsala ba sai ma inganta ta ɓangaren samar Yabanya mai kyau” inji Malam Auwal.

A cewar masanin tuni ƙasashe irin su Amurka , Australia da Afirka ta Kudu sai Brazil da Isra’ila dama India suka karbi tsarin tare da haɓɓaka shi a fannin Noma daban -daban, da hakan tasa kusan su ke Noma fiye da rabin abinda ake shukawa na fannin Cimaka a faɗin Duniya , kuma Nau’ikan Abincin su bashi da illa ga Lafiyar Ɗan Adam.

Masanin yace lokaci yayi da ya zama tilas ga Manoman ƙasar nan su bada himma wajen ƙarbar tsarin Noman domin samar da wadataccen abinci a ƙasar nan da kuma Yankin nahiyar Afirka ta Yamma , a ɓangare ɗaya kuma ya bunƙasa tattalin arzikin su.

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img