Masarar Rani tafi ta Damina kyau in an bata kulawa -Dr Muhammad Auwal

Must Try

Aminu Halilu Tudun Wada

Masani kana ƙwararre kuma Malami a sashen kula da tsirrai na tsangayar Aiyyukan Gona da ke Jami’ar Bayero , Dr Muhammad Auwal, ya ce Masara da aka shuka cikin kyakkyawar kulawa da Rani tafi ta Damina kyau.

A wata tattaunawa da yayi da Jaridar FARMERS VOICE NG, Dr Muhammad Auwal , ya bayyana cewar Noma na Masara a lokacin Damina na da Alfanu da ƙaruwa sosai ga Manoma matukar anbi matakan da suka dace na ƙwarewa ta Zamani da kuma tuntubar Masana to sai duk da haka Noman ta da Rani na fin na Damina saboda iya kula da Ruwa na ban Ruwa saɓanin yadda al’umma ba zasu iya sarrafa Ruwan Damina ba da yanayin da ta zo dashi.

” Noma na Rani na buƙatar shiri kamar kowanne Noma , haka zalika ita kan ta Masara , tilas Manomi yayi kyakkyawan tsari da tanadi , da tun da farko ya san ina zai yi Noman sa gurin ya dace ko akasin haka.Sannan me yake da shi a ƙasa na kuɗaɗen da zai kashe wajen Noman har zuwa lokacin da zai yi girbi da ajiya”.

” Rashin yin tanadin da tsarin ya na taka muhimmiyar rawa wajen yin asarar da Manoman mu ke yi, wanda in ka kwatanta da ƙasar da tafi Noma Masara a Afirka , wato Afrika ta Kudu (South Africa ), suna samun Tan (Ton) Goma da duk Kadada (Hectre ), sabanin mu da ake samun ƙasa da Takwas zuwa Bakwai , da in kayi duba da hakan tabbas koma baya ne da asara in aka duba yadda Noman yake a zamanan ce da kasuwar Duniya” inji Dr Muhammad Auwal.

Masanin ya ce ya zama wajibi ga gwamnatoci a dukkanin matakai a ƙasar nan da su samar da tsare -tsaren da za ake aiwatar dasu da zasu taimaka wajen kara bunkasa Noma na Masara da sauran dangogin su don bin sahun ƙasar Amurka da nahiyar Turai da suke Noma kaso 60 cikin 100, na Masarar a Duniya , da suka bar kaso 30 ga sauran ƙasashen Duniya.

Muhammad Auwal, ya ce samun ingantaccen iri na zamani mai yi da wurwuri da kiyayewa wajen biyan buƙatar Masara , saka taki akan lokaci shi ne zai bawa Manomi riba a noman.Bugu da ƙari kiyayewa da bin ƙa’idoji da iya sarrafa yanayi musamman ma Ruwa a lokacin Noman na Rani shi yake bawa Manoma Gwaggwaɓar Riba fiye da Noman na Damuna.

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img