Jihar Kano ta Buƙaci Gwamnatin Tarayya Ta Kaiwa Madatsun Ruwar Jihar Ɗauki

Must Try

Gwamnatin jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gyara wasu daga cikin madatsun ruwa da ke jihar wadanda ke da matsaloli, ta yadda za a inganta harkokin noman rani da wadata jihar da abinci.

Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi bakuncin ministan albarkatun ruwa Farfesa Joseph Terlumun Utsev,lokacvin da ya kai ziyara fadar gwamnatin jihar a ranar Laraba a yayin ziyarar aiki da ya kai wa gwamnan na Kano.

A cewar Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo y ace jihar ta Kano na da madatsun ruwa 21 wadanda ake amfani da su don noman rani a jihar.

A cewar Gwarzo wasu daga cikin madatsun ruwan na bukatar daukin gaggawa daga gwamnatin tarayya don gudun ballewar madatsun ruwan da ka iya jawo asarar rayuka da dukiyoyi a wasu sassa na jihar.

Ya ce wasu daga cikin madatsun ruwan sun fara tsatstsagewa wasu kuma sun fara cushewa don haka suna bukatar daukin gaggawa, don haka ne ma gwamnatin jihar a nata mataki ta kafa kwamiti da zai tattara bayanai kan halin da madatsun ke ciki.

Bayan bukatar kai daukin ga ministan albarkatun ruwan na Najeriya Gwarzo ya bayyana cewa madatsun ruwan na taka muhimmiyar rawa ga ci gaban tattalin arzikin jihar ta hanyar gudanar da noman rani da samar da ayyukan yi a tsakanin al’umma.

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img