Janye Tallafin Man Fetur: Farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi a Kano

Must Try

Abdulkadir Haladu Kiyawa

Hauhawar farashin kayan masarufi da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur a baya-bayan nan ya haifar da cece-kuce a tsakanin mazauna jihar Kano.

A ranar Laraba, 31 ga watan Mayun shekarar nan ta 2023 ne Kamfanin Mai na Najeriya (NNPCL), ya sanar da sake duba farashin man fetur, wanda a baya ana sayar da shi a kan Naira ₦260 amma yanzu ana sayar da kowacce lita kan Naira ₦560.

Sabon farashin da aka samu ya haifar da tashin gwauron zabi ga kayan abinci wanda a bayyane yake karara al’umma sun shiga matsi, musamman marasa galihu, wadanda su ke kokawa kan hauhawar farashin kaya a birnin na Kano.

Jaridar Farmers Voice NG ta lura cewa farashin kayan abinci na yau da kullun ya ƙaru matuƙa a manyan kasuwannin Kano.

Wani bincike da Jaridar Farmers Voice NG ta gudanar a kasuwannin birnin Kano ya nuna cewa farashin wasu kayayyaki ya rubanya bayan cire tallafin.

A kasuwar Tarauni, shinkafa ‘yar gwamnati da ake sayar da ita kan Naira 39,000 a yanzu ta kai Naira 42,000, yayin da sabuwar shinkafar gida ake sayar da ita tsakanin N34,000 zuwa N36,000.

A kasuwar Dawanau, buhun gero mai kwano 40, wanda a baya ake sayar da shi Naira 22,000 yanzu haka ya koma Naira 30,000 yayin da buhun masara mai kwano 40 da ake sayar da shi Naira 23,000 a yanzu ya koma Naira 34,000. Buhun Masara kwano 40, wanda a baya ana sayar da shi kan Naira 23,000 a yanzu ana sayar da shi kan Naira 34,000.

A ziyarar da Jaridar ta kai kasuwar kayan lambu ta Yankaba, an samu hauhawar farashin tumatur da barkono da albasa.

Jaridar Farmers Voice NG ta tattaro cewa matsakaicin kwandon Tumatir da ake sayar da shi akan Naira 5000 ya kai Naira 38,000 yayin da buhun albasa da ake sayarwa Naira 7000 yanzu ya kai Naira 15,000.

Barkonon da a baya ake sayar wa akan Naira 5000 zuwa Naira 6000, yanzu ya tashi zuwa Naira 15,000 da kuma Naira 23,000 ya danganta da wanne iri ne.

A kasuwar Sabon Gari, mun tattauna da wani mai sayar da kayan abinci Ibrahim Idris mai shekaru 35, ya shaida wa jaridar Farmers Voice cewa wannan lamari yana da matukar ban tsoro la’akari da yadda farashin kayan abinci ke karuwa a kullum, har ta kai masu sayan kayayyakin a kullum raguwa suke yi.

Ya ce, ‘’matsalar canjin kudaden ƙasashen waje na ci gaba da shafar farashin kayayyaki a kasuwanni, inda ya ce bayan cire tallafin man fetur al’amarin ya ƙara ta’azzara.

Wani dan kasuwar ma a kasuwar Sabon Gari wanda ya bayyana sunansa da Sani Makole, mai shekaru 47, ya ce yadda farashin kayan abinci ya rubanya a ‘yan kwanakin nan abin takaici ne.

Ya koka da cewa ‘’sakamakon hauhawar farashin kayan abinci, wasu masu sayan kayayyakin ba sa iya sayan adadin abincin da suka saba saya a baya’’.

Ya kuma yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da su ɗauki matakan da suka kamata wajen daƙile tsadar kayayyaki domin dakile illar cire tallafin man fetur.

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img