Har yanzu ba a kama hanyar bunƙasa noma ba a Najeriya – SEEDAN

Must Try

Ƙungiyar kamfanonin masu samar da iri a Najeriya wato Seed Entrepreneurs Association of Nigeria (SEEDAN), ta ce duk da ƙoƙarin da gwamnatoci ke yi wajen haɓaka ayyukan noma da samar da abinci a ƙasar, akwai abubuwan da ake yi tamkar barin jaki ne ana dukan taiki.

Ƙungiyar ta ce da gwamnatoci sun mayar da hankali kan samar da iri da yanzu ba wannan maganar ake yi ba a ɓangaren noma a ƙasar.

Cikin wata tattaunawa da BBC, shugaban ƙungiyar ta SEEDAN Yusuf Ado Kibiya, ya ce kowa ya san iri ƙwayace ƙanƙanuwa kuma a cikinta tana da komai tare da ita kamar abinci da makamantansu, sannan idan aka shuka ta aka ba ta ruwa za a ga shuka ta fito.

Ya ce, “Shi iri kala-kala ne, akwai iri na gargajiya wanda jama’a suka saba da shi, da kuma iri na zamani wanda ke taimaka wa manoma musamman wajen samun amfani mai inganci da yalwa.”

Ya ce, wannan shi ne dalilin da ya sa al’amura suka rincabe ake samun koma baya a harkar noma, sabanin a baya.

“ Babbar matsalar da Najeriya ke fuskanta ita ce ta zubar da abubuwan da ada ake amfani da su musamman kafin a yi amfani da iri, misali wajen binciken iri mai kyau da zai samar da ingantaccen amfanin gona mai yalwa, ko kuma irin da zai da ce da yanayin gonar da yawancin manoma a ƙasa ke amfani da ita.”

Yusuf Ado Kibiya, ya ce, “ Mu masu kamfanin iri muna sayen iri ne a wajen masu bincike sannan mu je mu shuka shi, saboda mun san duk irin da za mu siya an riga an san yanayinsa.”

Shugaban ƙungiyar kamfanonin masu samar da irin ya ce, ya kamata mutane su sani cewa shi kansa noman iri daban ya ke da noman da aka saba,don haka duk wani noma da za a yin a abinci idan ba ka da kyakkyawan iri to akwai matsala.

Ya ce, “Abin da ke janyo matsala ke nan a Najeriya yanzu, an daina amfani da irin da kamfanoninmu ke samarwa a harkar noma, shi ya sa abubuwa ke rincabewa.”

To amma da a ce ana amfani da irin da muke samarwar wanda aka yi bincike a kansa aka san amfaninsa, da tuni yanzu an wuce maganar samar da iri.

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img