Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin magance rikicin manoma da makiyaya

Must Try

Kwamishinan ƙasa da safiyo na jihar Kano, Adamu Aliyu Kibiya, ya bayyana kudirin gwamnatin jihar na magance rikice-rikicen da ake fama da su a tsakanin manoma da makiyaya a wasu sassan jihar.

Da yake jawabi a taron manema labarai a Kano, Kwamishina Adamu Aliyu Kibiya ya bayyana daya daga cikin abubuwan da ke ƙara rura wutar waɗannan tashe-tashen hankula a matsayin mamaye burtali da wasu ɗaiɗaikun mutane ke yi, wanda ke haifar da rashin jituwa tsakanin manoma da makiyayan.

Ya ƙara da cewa gwamnatin jam’iyyar NNPP ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta jajirce wajen ƙwato filayen kiwo da aka mamaye.

“Manufar farko ita ce samar da isasshen fili ga makiyayan da za su yi kiwo da kuma tabbatar da abincinsu,” in ji shi.

Kwamishinan ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na samar da dawwamammen zaman lafiya a rikicin manoma da makiyaya da ya kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a al’ummomi daban-daban a fadin jihar Kano.

An dade ana fuskantar rashin jituwa tsakanin manoma da makiyaya, inda manoman kan zargi makiyaya da kora dabbobi cikin gonakinsu suna yi masu ɓarna.

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img