Farashin shinkafa zai ƙaru da kaso 32 a shekarar 2024 – Rahoton AFEX

Must Try

Ana hasashen farashin shinkafa a Najeriya zai karu da kashi 32 cikin 100 a shekarar 2024, a cewar rahoton noman damina na kwanan nan na AFEX.

Sai dai rahoton ya bayyana cewa ana sa ran noman shinkafa zai karu da kusan kashi hudu cikin dari.

“Yayin da ake sa ran karuwar noman da kusan kashi 4 cikin dari, muna sa ran za a iya samun hauhawar farashin sharerar shinkafa da kusan kashi 32 cikin dari,” in ji rahoton na AFEX

Rahoton ya alakanta hasashen karuwar noman da rashin ambaliyar ruwa a shekarar 2023.

A halin da ake ciki kuma, rahotannin sun bayyana cewa buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50 ya tashi daga zuwa matsakaicin farashin N12,000 zuwa N55,000 daga shekaru goma da suka gabata.

Wannan ci gaban ya zo ne yayin da hauhawar farashin abinci a Najeriya ya karu zuwa kashi 31.52 a watan Oktoban 2023 daga kashi 30.64 a watan Satumbar 2023, a cewar sabon rahoton hukumar kididdiga ta kasa.

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img