Abincin da ake nomawa a yankin Arewa zai ciyar da Najeriya – Shugaban Jami’ar FUD

Must Try

Shugaban Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Dutse, a jihar Jigawa Farfesa Abdulkarim Sabo Muhammad, ya bayyana irin damarmakin da Arewacin Najeriya ya ke da shi wajen noma abincin da zai ciyar da al’umma ƙasar nan baki ɗaya.

Farfesa Abdulkarim Sabo ya ce Najeriya ta na da hanyoyin kasuwancin kayan abincin tsakanin ƙasashen duniya.

Tun da farko shugaban Jami’ar ta FUD ya bayyana haka ne a taro karon Farko da Masana kimiyyar Abinci Suka gabatar a jami’ar Bayero da ke Kano.

Taken taron na bana dai shi ne “Samarwa Abincin da ake Nomawa a Arewacin Najeriya Gurin Zama a Kasuwanni Duniya”.

Farfesa Abdulkarim ya ce Najeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen da ake alfahari da ita a Nahiyar Afrika dama duniya baki ɗaya da ta ke da albarkar ƙasar noma.

Farfesa ya bayyana irin yadda masana daga ko’ina a faɗin duniya su ke gabatar da ƙasidun albarka noma da kasar take dashi kama daga noman Masara da Dawa da Gero da kuma Maiwa.

“Wanda da a ce shugabannin ƙasar nan za su haɗa hannu da masana, cikin ƙanƙanin lokaci ƙasar za ta zama abar kwatance a duniya dama samun hanyoyin shigowar kudi ga ƙasar.

Ana ta Jawabin Shugaban Kungiyar Masana Kimiyyar Abinci ta Arewaci Maso Yammacin Najeriya, Dr. Zahra’u N. Bamalli, ta bayyana cewa manufar taron na bana shi ne shigo da masana kimiyyar Abinci daga ko’ina a faɗin Arewacin ƙasar domin haɓaka yankin gaba.

Dr. Zahra’u N Bamalli ta ƙara da cewa, tun asalin Arewacin Najeriya yana da tarin abinci wanda ake yi su tun iyaye da kakanni, wanda ya zama dole ga masana su rinƙa yin nazari dama fito da amfanin su domin ingantawa gami da gogayya da sauran taƙwarorinsu na duniya.

“Ya zame mana dole mu rinka inganta abincin gargajiya tare da shigo da dabarun alkinta yadda ake yinsu, domin kula da lafiya al’ummar dama ka re su daga barazanar kamuwa da cututtuka wanda aka iya kamuwa ta hanyar rashin inganci abinci.

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img