Yadda tsuntsaye jan baki su ka yi wa manoma ta’adi a jihar Kebbi

Must Try

Wani faifen bidiyo na baya-bayan nan da aka wallafa a shafin Twitter na Gidan Talabijin na Najeriya wato NTA, ya nuna yadda tsuntsayen Quelea da aka fi sani da jan baki su ka yi wa manoma ɓarna a jihar Kebbi, lamarin da ya janyo musu asara mai yawa.

Lamarin dai ya ƙara ta’azzara yayin da kusan hekta 75,000 na noman shinkafar rani a Argungu da ke Jihar Kebbi, ta sasanta sakamakon mummunar ɓarnar da tsuntsayen jan baki su ka yi

Tasirin mamayar tsuntsayen na jam-baki ya yi wa manoma ta’annati, inda da yawa cikinsu tuni suka bayyana gagarumar asarar da suka tafka a gonakinsu.

Manoma a Najeriya dai na fuskantar matsalolin tsuntsaye jan baki da farin dango da ƙarancin ruwan sama, abin da kan haifar da tsadar abinci

Haka kuma a shekarar 2021, Hukumar Samar da Abinci da Aikin Gona ta Majalisar Dinkin Duniya FAO, ta yi kiyasin cewa ana rasa amfanin gona ta dalilin tsuntsaye a kowace shekara da ya kai $50m, musamman ma a yankin sahara na Afirka.

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img