Yadda ake amfani da Fitsarin Zomo wajen kashe ƙwari a ‘Gona’

Must Try

Fitsarin zomo yana ƙunshe da abubuwa kamar haka:

1. Taki Mai Ɗauke da sinadaran NPK. (Nitrogen, Phosphorus, Potassium)

2. Yana Ɗauke da maganin Ƙwari (Biopesticide) wanda yake kashe, Aphids, Whiteflies, Caterpillars.

Yanda ake Amfani Fitsarin Zomo a Gona

1. Fesawa shuka (spray) ake. Ka tabbatar ka jijjiga shi sosai kafin a fesawa shuka.

A yanzu haka a kasuwa ana siyar da litre ɗaya ta fitsarin zomo akan kudi Naira 600 zuwa Naira 700.

Sannan shi wannan fitsarin zomon ba shi da wata illa ga lafiyar shuka ko kuma ga muhalli, ko kuma ga kai me fewasar.

2. Ana sirka shi wannan fitsarin zomon akan ratio 1:5 (Ma’ana idan ka sa litre ɗaya ta fitsarin zomo, sai ka sa litres biyar na ruwa), sannan sai a girgiza shi sosai. Daga haka ka kammala haɗashi sai feshi.

A maimakon amfani da magungunan feshi na bature, zaku iya yin amfani da wannan fitsarin zomon.

A shekarar 2021 Hukumar Bunkasa Harkar Noma ta Kasa (NALDA) ta fito da wani shiri kan masu kiwon zomo, inda hukumar ta dauki masu kiwon zomo dubu 17 daga Kudancin Najeriya, tare da raba musu zomaye dubu biyar a jihohin Imo da Abiya da Kurosriba da Oyo a kashin farko na shirin.

Matasan da shirin ya dauka domin koya musu kiwon sun bayyana cewa su na samun kudi daga kiwon inda akalla suke samun kimanin Naira dubu 100 daga kashi da fitsarin zomayen da suke sayarwa duk wata.

Ibrahim Lawan Musa

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img