Najeriya na shirin fa ra yiwa dabbobi riga -kafin cutar Anthrax

Must Try

Najeriya na shirin yi wa dabbobin ƙasar huji ko riga-kafin cutar Anthrax bayan ɓullar cutar a wata gona da ke Suleja a jihar Niger kamar yadda gidan rediyon BBC Hausa ya rawaito.

Ma’aikatar noma a Najeriya ta ce ta ɗauki matakan da suka dace don daƙile cutar da hana yaɗuwarta, kuma gonar da ake magana, wadda ake kiwon shanu da tumaki da Awaki, har ta ɗauki matakan keɓe ta tare da sa’ido a kan ta.

Tun a watan Yunin da ya wuce, gwmanatin Najeriyar ta ankarar da al`ummar ƙasar game da ɓullar cutar a ƙasashen Ghana da Burkina Faso da kuma Togo. Wannan ne ma ya sa mahukunta suka gargaɗi al`umma da suke dinga ɗaukar matakan kariya.

Wani kwararren likitan dabbobi a Najeriya, Dakta Abubakar Sulaiman, ya ce duk da cewa cutar ba ta da saurin yaɗuwa, amma bil`adama ma kan harbu da ita idan ya ci nama ko gogayya da jikin dabbar da ta harbu.

Ya ce ɗaya daga cikin manyan hanyoyin kariya daga cutar, ita ce yi wa dabbobi huji kamar yadda mahukunta a Najeriyar suka yi aniya.

A ƴan makwannin da suka wuce ne aka samu labarin ɓullar cutar a ƙasashen Ghana da Burkina Faso da kuma Togo.

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img