Matsalolin tsaro ka iya kawo koma bayan Harkokin Noma a Zamfara

Must Try

Manoma a jihar Zamfara na cikin fargabar yin noma a shekarar bana, saboda ƙalubalen tsaro da jihar ke cigaba da fuskanta.

Daya daga cikin manoma a karamar hukumar Maru, Musa Garba, ya ce a duk shekara yana girbe buhunan shinkafa sama da 100 da buhun gero 50, sai dai ya koka da cewa har yanzu bai yi shuka ba a bana saboda tsoron ‘yan fashin daji da kullum suke mamaye gonaki domin sacewa ko kashe manoma.

Shi kuwa wani manomi Sani Musa ya ce ya yanke shawarar yin shuka a bana saboda tunanin cewa gwamnati mai ci za ta dauki mataki cikin gaggawa kan matsalar tsaro. Sai dai ya koka da yadda ‘yan fashin daji suka lalata amfanin gonakin.

Jaridar Punch ta rawaito cewayanzu hakan anyi watsida sama da kashi 70 cikin 100 na filayen noma a jihar saboda fargabar ayyukan ‘yan bindiga.

Matsalar tsaro na daga cikin abubuwan da ake hasashen za su haddasa ƙarancin abinci a arewacin Najeriya saboda yadda yan fashin daji da masu garkuwa ke addabar manoma suna hana su nome gonakinsu

Ana ganin ƙalunbalen tsaro da manoma ke fuskanta zai yi tasiri ga samar da abinci a Najeriya.

Al’umma a Zamfara sun daɗe suna fuskantar hara-haren tare da ƙone garuruwansu daga ƴan fashi masu ɗauke da manyan bindigogi.

Hukumomi da jami’an tsaron sun sha iƙirarin cewa suna kokarin ganin an shawo kan matsalar da magance ta baki daya, amma har yanzu ana kai hare-hare da garkuwa da mutane duk da ikirarin gwamnatin Zamfara na yin sulhu da ƴan fashin.

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img