Babu barazanar yunwa ga jihohin Arewa maso gabashin Nigeria – Gwamna Zulum

Must Try

Aminu Halilu Tudun Wada

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane sama da Miliyan 4 ne ke fama da matsananciyar yunwa a jihohin Borno, Adamawa da Yobe, a Arewa maso gabashin Najeriya.

Babban jami’in jin kai na hukumar a kasar nan Mathias Schmale, ya bayyana haka ga manema labarai a birnin Geneva na ƙasar Switzerland, a wani taron ƙasashen Duniya na samar da wadataccen Abinci.

Ya ce adadin yara ƴan ƙasa da shekaru biyar da ke fama da tsananin rashin abinci mai gina jiki ya ruɓanya a cikin shekara guda zuwa 700,000.

A cewar babban jami’in na Majalisar lamarin ya samo asali ne sakamakon rashin tsaro sama da shekaru 10 da suka gabata sakamakon hare haren ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP, da ke hana mutane noma da samun kuɗin shiga daga filayen noma.

To sai dai a wani martani na musanta hakan , gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce ana kara kakkabe karfin ‘yan ta’adda da hakan ke bada dama ga Manoma komawa gonakin su don yin Noma.

Zulum , ya bayyana hakan ne a birnin Ndjamena na kasar Chadi , a wani taron Gwamnonin yankin Tafkin Chadi da suka gudanar akan matsalolin tsaro dake damun yankin da kuma zummar farfaɗo da Tafkin na Chadi , don kara habbaka harkokin Noma na Rani da Damina tare da Kiwo.

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img