Ambaliya ta kashe mutum uku a Kebbi Ambaliya

Must Try

Mutum uku sun rasu sakamakon mamakon ruwan sama da aka samu a yankin Dakingari na karamar hukumar Suru na jihar Kebbi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Shugaban karamar hukumar ta Suru, Muhammad Lawal na cewa ruwan ya yi ta zuba na sa’o’i da dama, inda ya kuma lalata kayayyaki na miliyoyin naira.

Muhammad ya ce bayan mamakon ruwan saman, ruwa ya yi ta kwarara daga kan duwatsu kusa da garin Dakingari wanda yana cikin abubuwan da suka haddasa ambaliyar.

“Sama da shekara ashirin, muna fama da ambaliya kowace shekara. Gwamnatocin da suka gabata sun gina magudanan ruwa a garin domin magance matsalar, amma hakan bai sanya an daina samun ambaliyar ba,” in ji shi.

Ya bayar da shawarar cewa za a iya magance matsalar ta ambaliya idan aka samar da shingaye kusa da duwatsun.

Ya yi kira ga mutanen yankin da su daina gini kusa da magudanun ruwa da kwalbatoci, inda ya kuma ce ya su guji zubar da shara a ko’ina.

Jihohi 19 da ke fuskantar barazanar ambaliyar ruwa a Nijeriya

‘Ambaliyar ruwa ta tafi da matata da ƴaƴana 13’

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img