Kamfanin WACOT, mai samar da kayan aikin noma da kuma cibiyar Nazari da bincike akan harkokin noma a yankuna masu karancin albarkatun ruwa ta Jami’ar Bayero da ke Kano wato CDA, sun sanya hannu a bisa wata yarjejeniyar samar da kwalejin koyar da dabarun noman Riɗi a garin Gumel da ke jihar Jigawa.
A cikin shekaru huɗu masu zuwa ana sa ran yarjejeniyar za ta samar da yin aiki tare da kuma horar da manoman Riɗi ta hanyar ba su horo na musamman tare da ƙara musu sani akan harkar noman Riɗi a zamanance tare kuma da ba su shaidar halartar kwalejin.
Habiba Suleiman, daga kamfanin WACOT ta bayyana farin cikin ta game da wannan yarjejeniyar tare da yaba ƙoƙari tare da ƙwarewar cibiyar Nazari da bincike akan harkokin noma a yankuna masu karancin albarkatun ruwa ta Jami’ar Bayero.
Ta ce “Wannan yarjejeniyar ta na nufin samar daliban da suka kammala samun horo na musamman akan noman Riɗi, wanda zai haifar da ƙaruwar yawan amfanin gona da kuma samun kyakkyawan sakamako musamman bunƙasa tattalin arzikin manoman da kuma ƙasa baki ɗaya”
A nata ɓangaren mataimakiyar daraktar cibiyar ta CDA, Farfesa Amina Mustapha, Jami’ar ta Bayero da kuma cibiyar Nazari da bincike akan harkokin noma a yankuna masu karancin albarkatun ruwa wato CDA, sun yi farin ciki da wannan yarjejeniyar la’akari da dacewa da manufa da ƙudurin cibiyar.
Ta ce “Mun ji daɗin wannan yarjejeniya da kamfanin WACOT, saboda ta dace da hangen nesa na Cibiyar CDA na samar da tsarin cigaba mai ɗorewa ta hanyar haɗin gwiwar manoma da kuma kamfanoni masu zaman kansu.”
Ana sa ran kwalejin koyar da dabarun noman Riɗin za ta samar da manoman da za su noma Riɗin da za a fitar da shi ƙasashen da su ke nahiyar Amurka da sauran kasashen duniya.
Masu kula da lamura a ɓangaren aikin noma, na nanata buƙatar samar da yanayin haɗaka na yin aiki tare tsakanin kamfanoni masu sarrafa kayayyakin abinci da kuma cibiyoyin bincike da nazarin dabarun noma a matsayin matakin bunƙasa ƙasa da abinci.