NDE ta rabawa Manoma fiye da ₦ Miliyan 1 a matsayin lamuni marar ruwa a Kano

Must Try

Hukumar samar da ayyukan yi ta ƙasa (NDE) ta ɗauki matakin rage zaman kashe wando a jihar Kano ta hanyar raba jumillar kudi kimanin Naira miliyan 1.9 a matsayin lamuni mai sauki ga manoma 19 da suka ci gajiyar shirin a karkashin shirin samar da aikin yi mai ɗorewa na shekarar 2023.

Rarraba kudaden wanda aka gudanar a jiya Laraba a birnin Kano, ya kasance karkashin Sashen inganta aikin yi a yankunan Karkara (REP) na hukumar ta NDE. Manufar wannan shiri dai ita ce magance ƙaruwar rashin aikin yi a Najeriya.

Malam Abubakar Fikpo, Darakta Janar na hukumar NDE, ya jaddada cewa shirin ya mayar da hankali ne wajen horar da matasa marasa aikin yi a fannoni daban-daban da suka hada da samar da kayayyaki da adanasu tare da sarrafa da kuma aikin alkintasu waje guda.

Tun da farko an zaɓo waɗanda suka ci gajiyar su 19 daga rukunin mutanen da aka horar a karkashin shirin na REP a cikin jihohi 12. Kuma za a raba Naira miliyan 22.8 ga mutane 228 daga wadannan jahohin domin su samu damar kafa ƙananan sana’o’in masu alaƙa da noma.
Hakazalika Mista Fikpo, ya ƙara da cewa lamuni marar ruwa zai ƙara musu ƙwarin gwiwar yin amfani da damar yadda ya kamata tare da biyan bashin cikin wa’adin da aka ƙayyade, yana mai jaddada cewa nasarar da suka samu za ta ba da dama ga sauran matasa marasa aikin yi su ci gajiyar shirin.

Mista Emem Duke, Daraktan REP, ya bayyana cewa, shirin rancen an yi shi ne domin karfafawa waɗanda suka ci gajiyar tallafin, ta yadda za su kafa sana’o’in da za su dogaro da kansu.

A lokacin taron da ke da nufin wayar da kan wadanda suka ci gajiyar rancen yadda ya kamata, mataimakin daraktan hukumar ta NDE, Joshua Fagbemi, wanda ya samu wakilcin Malam Abubakar Fikpo ya ce za a rana rancen ne ga waɗanda suka ci gajiyar ta asusun bankunansu.

Wasu daga cikin waɗanda suka ci gajiyar tallafin sun nuna jin dadinsu ga hukumar ta NDE bisa wannan damar da ta ba su, kuma sun bayar da tabbacin za su yi amfani da kuɗaɗen ta hanyar da ya kamata.
.

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img