Manoma a Kano sun koka kan tsadar takin zamani

Must Try

Manoma a ƙananan hukumomin Ungogo da Kumbotso a jihar Kano, sun bayyana cewa tsadar takin zamani da man fetur a bana na iya haifar da ƙarancin kayan amfanin gona da kuma tsadar kayan abinci.

Abdullahi, mai shekaru 56 manomi a yankin Panisau Bayan Gari, da ke karamar hukumar Ungogo, ya bayyanawa manema labarai yadda tsadar takin ta yi matuƙar tasiri a harkar nomansa sama da shekaru 4.

A cikin kalamansa: “Ina da kadada mai girma wadda nakan shuka gero a lokacin damina. A da, lokacin da taki ke kan Naira 4,000 zuwa Naira 5,000, na kan girbe buhunan gero sama da 60.

“Amma yanzu da ƙyar nake girbar buhun gero 20 saboda tsadar takin zamani domin yanzu ana sayar da taki samfurin Urea tsakanin ₦18,000 zuwa ₦21,000″

Umar Salim, mai shekaru 40 manomi a yankin Agalawa da ke ƙaramar hukumar Ungogo ya jaddada cewa noma na ƙara wahala a kowacce rana domin yawancin manoman talakawa ne.

“Mafi yawan manoman kauyen ba sa iya noma saboda ƙarancin jari, mu manoma na gaske da masu gonakin yanzu mun zama ma’aikata ga manoman birni waɗanda suka yi hayar gonakinmu. Hakan na faruwa ne saboda tsadar kayan amfanin gona kamar takin zamani da man fetur,” in ji shi.

Haka lamarin yake a wasu al’ummomin ƙaramar hukumar Kumbotso yayin da wasu manoman suka koka kan irin kalubalen da suke fuskanta wanda ke hana masu ruwa da tsaki damar cimma burin da suke so.

Abdullahi Nura mazaunin ƙauyen Dan Danko da ke ƙaramar hukumar Kumbotso ya bayyana cewa gonarsa ta shinkafa tana fama da rashin taki da karancin ruwan sha.

“Ya kamata in sanya akalla buhu 1 na Urea da takin Kampa guda 1 a wannan filin noma, amma saboda tsadar takin, sai na yi amfani da rabin buhun takin guda biyu kacal kuma wannan zai yi. Ya yi tasiri sosai ga yawan amfanin gonar da ake nomawa.”

“A yanzu haka ina kashe Naira 12,000 wajen sayen mai a duk kwanaki 4 domin yin ban ruwa a gonar shinkafata”

“A baya, Naira 2,500 kawai nake kashewa wajen yiwa gonar shinkafata duk bayan kwanaki 4. Farashin takin zamani da man fetur ya na matuƙar wahala,” Nura ya kara da cewa.

A wani bincike kan farashin taki a wasu daga cikin kananan hukumomin da ke jihar Kano, ya nuna cewa farashin takin NPK ya tashi daga ₦25,000 zuwa 30,000. Kuma farashin buhun takin NPK mai nauyin kilogiram 50 ya tashi daga ₦26,000 – ₦30,000, ya danganta da kasuwar da manomi yake siya.

Ana siyar da buhun taki mai nauyin kilogiram 50 na NPK 15:15:15 akan ₦28,000 – ₦30,000 da buhun 50kg na NPK 12:12:17 taki tsakanin ₦25,000 – ₦29,000 wannan kuma ya dogara da kasuwa.

Sai dai a kasuwar Sabon Gari da ke cikin birnin Kano, ana siyar da farashin 50kg NPK 15:15:15 akan 29,600.00, yayin da 50kg NPK 12:12:17 ake siyar da shi 29,500.00 da 50kg NPK 20:10 26,000.00.

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img