HausaLabarai

Gwamnatin Najeriya na shirye – shiryen haramta safarar masara zuwa ƙetare

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da wani kudirin doka da ya haramta fitar da duk wata masara mai yawa da ba a sarrafa ta ba daga ƙasar nan kamar yadda kamfanin dillancin Labarai an Reuters ya rawaito.

Najeriya dake a matsayin ƙasa mafi yawan jama’a a Afrika na fama da matsalar tsadar rayuwa da ba a saba ganin irinta ba a ckin gwamman shekaru.

An shiga matsin tattalin arziƙi tun bayan shugaba ƙasar Bola Tinubu ya ɗauki wasu tsauraran matakan da suka haɗa da ƙarya darajar kuɗin ƙasar na naira kan dalar Amurka da kuma kawo ƙarshen tallafin man fetur da ma tsadar man fetur a ƙasar.

Karyewar darajar Naira ta sanya ƴan Najeriya fitar da kayan abinci kamar masara shinkafa da dawa, saboda ribar da suke samu idan suka karbo kuɗin makwaftan kasashe.

Masara na cikin jerin hatsin da ake yawan amfani da shi a Najeriya. musamman wurin abincin dabbobi da ababen sha da kuma samar da gari.

Sashin kula da ayyukan noma na ƙasar Amurka USDA ya yi hasashen samun ƙaruwar masarar da ake fitarwa a Najeriya daga metric tan dubu 50 a 2023/2024 zuwa metric tan dubu 75 a 2024/205.

Ƙudirin dokar na majalisar datttawan Najeriya na buƙatar amincewa da kuma sa hannun shugaban ƙasar kafin ya zama doka, kuma da zarar ya amince to fitar da masarar da ba a sarrafa ba zai haramta a ƙasar, kuma adadin da ake fitarwa zai zama metric tan 1.

Duk wanda aka kama da karya dokar zarar shugaban ƙasar ya amince da ita to za a yanke masa hukuncin zaman shekara 1 a gidan yari ko kuma kwace masarar da yake shirin fitar da ita ƙasar waje.

Wani rahoton haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin Najeriya da majalisar ɗinkin dunya ya ce, a watan Nuwamba mutum miliyan 30 ka iya fuskantari ƙarancin abinci a shekara mai zuwa, adadin da ya ƙaru da ɗaya bisa 3 na abinda aka gani a baya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button