Wani Manomi a Kano ya bayyana yadda manoma za su kare gonakinsu daga mamayar Tsuntsaye

Must Try

Abdulkadir Haladu Kiyawa

Wani manomi a jihar Kano, ya bayyana cewa tsarin amfani da sange yana inganta noman shinkafa matukar ta hanyar kare gonaki daga matsalar mamayar tsuntsaye.

Malam Sabiu Abubakar, mai shekaru 51, dake noma abubuwa da dama wanda kuma shi ne sakatare janar na kungiyar manoma ta Tanawa, ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da ya yi da jaridar Farmers Voice a ranar Lahadi.

Ya ce ”tsuntsaye da kwari suna da hatsari ga gonaki kuma a duk lokacin da suka mamaye gona, za su iya shafe amfaninta cikin ‘yan mintuna ko sa’o’i ya danganta da yawan su”.

A cewar sa, matsalar tsuntsayen, ”a wasu lokutan shi ne babban abin da ke haddasa karancin abinci ba a Kano kaÉ—ai ba har ma a Najeriya baki daya”.

Ya shawarci manoman shinkafa da alkama musamman a lokacin rani da su yi amfani da dabarun domin kare gonakinsu daga barazanar mamayar tsuntsaye.

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img