Jami’ar yaɗa ilimi da wayar da kai na Manoma daga Gidauniyar wayar da kan Manoma ta ƙasa wato ‘East -West Seed Knowledge Transfer Foundation Nigeria’ ƙarkashin hukumar Noma ta HortiNigeria, Amina Ado Yahaya , ta ce yin amfani da sababbin dabarun Noma na Zamani na daga cikin hanya mafi inganci da tasiri wajen takaita yaduwar cututtukan da suke addabar kayan amfanin gona na Manoma.
Amina Yahaya , ta bayyana hakan ne a taron kwana guda na wayar da kan Manoma da Jaridar al’amuran da suka shafi harkokin Noma ta FARMERS VOICE NG, ta re da hadin gwiwar cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da cigaba ta CITAD tare da Maɗaba’ar Fombina da rukunin gonakin Fombina suka shiryawa Manoma kan matsalolin karewa da takaita ƙwari da cututtukan dake damun shukoki musamman ma Tumatir , sai ban Ruwan Noman Rani na zamani da Noman Rufewa da killacewa na zamani wato ‘Green House Crop production’ da aka gudanar a makarantar Firamare dake Bunkure Gabas , a karamar hukumar ta Bunkure a Kano.
A cewar jami’ar amfani dabarun Noman zamani na bada tazara tsakanin shukoki da amfani da ingantaccen iri tare da amfani da magunguna masu inganci bisa shawarar Malaman Gona , a ɓangare ɗaya tare da sauya kayan amfanin gona da ake shukawa daga shekara zuwa shekara da hakan tace zai matukar tasiri wajen takaita kwari , da cututtukan dake damun shuka.
A jawaban su daban -daban , Malam Abdullahi Muhammad Babayaro daga Gidauniyar ta East -West Seed Knowledge Transfer Foundation da Injiniya Ibrahim Abubakar na cibiyar nazarin ƙasashen dake da ƙamfar Ruwa ta jami’ar Bayero wato CDA, sun yi karin haske kan amfani da hanyoyin dabarun Noma ta amfani da Zamani da Gargajiya da yadda ake gano matsalolin ƙwaruka kafin suyi Illa ga shuka.
Haka zalika sai yin amfani da sabuwar hanyar noman Rani na takaita amfani da Ruwa ta fasahar ɗigar Ruwa akan shuka ko kuma feshin sa , wato ‘Drip Irrigation and Sprinkler’ cikin Noman killacewa na ‘