Matuƙar gwamnati za ta tallafa mana, zamu iya samar da abinci ga Najeriya – Manoman Shinkafa

Must Try

Daga Abdulkadir Haladu Kiyawa

Manoman shinkafa a karamar hukumar Kura ta jihar Kano sun jaddada aniyar su ta samarwa da ƙasar nan wadataccen abinci, tare da yin korafi bisa yadda suka ce ana nuna musu wariya a wajen rabon taki ga kuma rashin samun tallafin noma daga gwamnati.

Karamar hukumar Kura dai dake kudu da birnin Kano, tana da tazarar nisan kilomita 30 daga ƙwaryar birnin jihar.

Da yake zantawa da wakilin Jaridar Farmers Voice NG, Shugaban Manoman Tukuba Multipurpose, Malam Ahmed Jinjiri Kura, ya bayyana cewa Allah ya albarkaci Nijeriya da kasar noma mai dimbin yawa a fadin jihohin Arewa da suka hadar da Yobe da Katsina da Kano da Zamfara da kuma Bauchi, da sauransu.

Shugaban ƙungiyar manoma ta Tukuba Farmers Multipurpose, Malam Ahmed Jinjiri Kura
Shugaban ƙungiyar manoma ta Tukuba Farmers Multipurpose, Malam Ahmed Jinjiri Kura

A cewar Jinjiri, noma shi ne kashin bayan ci gaban ƙasashen duniya masu karfin fada a ji, domin idan babu abinci babu wanda zai iya samun ci gaba ta ko wanne bangare.

Ya ce kasashe irin su China sun rungumi noma ne kafin fasaha duk da yawan al’ummar da suke da shi.

Ya kuma bayyana cewa a Kura, kadada daya a gona na iya samar da kusan buhun shinkafa 40, inda ake sayar da kowanne buhu tsakanin Naira 27,000 zuwa Naira 28,000.

Ahmed ya koka da cewa farashin da aka ambata a baya yana fuskantar tasgaro a yanzu sakamakon hauhawar farashin kayayyaki a kasuwa.

Jaridar Farmers Voice NG ta tattaro cewa manoman shinkafa a Kura suna sayar da amfanin gonakinsu a cikin gida a kasuwannin Dawanau da Kwanar Dan Gora da Bichi da wasu kasuwannin jihar Kano.

A kasuwannin waje kuwa suna sayar wa a garuruwa kamar Legas da Benuwe da Fatakwal da Ibadan da Owerri da Anambra, da sauransu.

Dangane da matsalolin da suka fuskanta a lokacin da aka bullo da tsarin taƙaita zirga-zirgar kudi a hannun jama’a kuwa, Malam Ahmed ya ce, “Mu manoman gida mun sha wahala matuka saboda ba mu yarda da hada-hadar kasuwanci ta kafar internet ba.

“Mun gwammace yin mu’amala da tsabar kudi, saboda hada-hadar kuɗi ta Internet ta fuskanci matsaloli a wancan lokacin” inji shi.

Da aka tambaye su kan yadda suke tafiyar da harkokin noman su a wannan lokaci da aka da cire tallafin man fetur, da kuma yadda zasu sayar da shinkafar su idan sun girbe, Jinjiri ya bayyana cewa ba su girbe amfanin gona a yanzu ba, don haka har yanzu ba su ji tasirin hakan ba.

Wata Gonar Shinkafa a ƙaramar hukumar Kura da ke jihar Kano
Wata Gonar Shinkafa a ƙaramar hukumar Kura da ke jihar Kano

Da aka tambaye shi kan hanyoyin sadarwar tallata kayayyaki na zamani, Malam Ahmed ya bayyana cewa tuni an riga an bar manoman shinkafa na Kura a baya wajen amfani da kafafen sada zumunta na zamani domin tallata kayansu.

Jaridar Farmers Voice NG ta gano cewa ƙungiyar su Ahmad Jinjiri, ta Tukuba Farmers ba ta samu tallafin gwamnatin tarayya ba tsawon shekaru takwas, sai dai babu tabbas ko kungiyar manoman Shinkafa ta Najeriya (RIFAN) ita ma bata samu tallafin ba tsawon shekaru takwas.

Da yake magana kan sake bude iyakokin ƙasar nan, Shugaban kungiyar AGOLAS Malam Adamu Muhammad, ya bayyana cewa ba shi da wata matsala da hakan.

Ya bukaci gwamnati mai ci da ta aiwatar da shirye-shiryen da za su rage kalubalen da manoma ke fuskanta a kasar nan.

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img