Gwamnatin ƙasar Norway ta bada ƙarin Dala miliyan 4.5 domin tallafawa ayyukan agaji na hukumar kula da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya FAO, domin magance matsalar da ta kunno kai a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Wakilin hukumar kula da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya FAO a Najeriya da kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, Fred Kafeero, ne ya bayyana haka a lokacin rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin hukumar ta MDD da gwamnatin Norway a birnin tarayya Abuja.
Kafeero ya ce tallafin da gwamnatin ƙasar Norway ta bayar ya kai dalar Amurka miliyan 24, tun farkon rikicin Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya, kuma sama da mutane miliyan ɗaya waɗanda rikici ya shafa sun amfana da tallafin.
A cewarsa, tun daga shekarar 2017, gwamnatin ƙasar Norway, ta hannun ma’aikatar harkokin wajen kasar, ta ba da gudummawa sosai wajen sake gina rayuwar al’ummomin da suka fi fama da rauni a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, wadanda sama da shekaru goma ke fama da rikicin Boko Haram.
Tallafin kuɗin dai za a yi amfani da shi wajen aiwatar da ɗorewar ayyukan da ake yi domin inganta samar da abinci mai gina jiki tare samar da rayuwa mai inganci a jihohin Borno da Adamawa da Yobe da kuma jihar Taraba.