Za a fuskanci ƙarancin abinci nan da watanni uku masu a Najeriya – Attahiru Bafarawa

Must Try

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, kuma mamba a kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya nuna damuwarsa kan ƴan fashin daji da ke addabar yankin Arewa maso Yamma da kuma Arewa maso Gabas, inda ya ce hakan na haifar da babbar barazana ga samar da abinci a Najeriya.

A cewarsa, maimakon maganar nade-naden ministoci, da cire tallafin man fetur, da kuma batun tattalin arziki, kamata ya yi gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta baiwa ɓangare samar da abinci ga ƴan Najeriya fifiko na musamman.

Dattijon ya kuma yi gargadin cewa idan ba a ɗauki tsauraran matakan dakile tashe-tashen hankula ba, yankin Arewacin Najeriya zai fuskanci koma-baya mai girman gaske a ɓangaren ilimi.

Bafarawa, wanda ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da jaridar The PUNCH, ya ce an rufe makarantun firamare da sakandare da dama a Arewacin Najeriya saboda ayyukan ‘yan bindiga, yana mai cewa, “Wannan babban bala’i ne.”

Ya ce, “Maimakon maganar ministoci, cire tallafin man fetur, da tattalin arziki, kamata ya yi gwamnati ta yi la’akari da samar da abinci domin a halin da muke ciki, nan da watanni uku masu zuwa, tabbas za mu fuskanci matsaloli a Najeriya, musamman a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya”.

“’Yan fashin sajin sun ƙi barin manoma su yi noma. Wannan lamari dai yana da matuƙar haɗari, ba wai kawai yadda ƴan fashin daji ke kashe mutane ba, har ma da yadda matsalar ƙarancin abinci za ta yi ƙamari a ƴan watanni masu zuwa, musamman a yankin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas. Don haka muna son gwamnati ta farka ta yi wani abu a kai.

“Ya kamata gwamnati ta yaki matsalar rashin tsaro da matsalar ƙarancin abinci a fadin ƙasar nan, domin lamari ne mai tsanani. Duk abin da wani shiri da gwamnati za ta zo da shi ya kamata a baiwa ɓangaren samar da abinci fifiko mai yawa” In ji Attahiru Bafarawa.

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img