Mai martaba Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta samarwa da manoma takin zamani a farashin mai rahusa.
Sarkin ya yi wannan kiran ne a yau Asabar a lokacin ya kai ziyarar gaisuwar Sallah ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a fadar gwamnatin jihar kamar yadda muƙaddashin sakataren yaɗa labarai na Gwamnan, Hisham Habib ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.
Da yake ƙarin haske kan muhimmancin bunƙasa noma, Sarkin ya jaddada wajabcin tabbatar da ganin manoma sun samu takin zamani a farashi mai sauki, ta hanyar baiwa manoma tallafin kuɗi tare da inganta harkokin noma a jihar Kano.
Bugu da ƙari, a lokacin ziyarar, Sarkin ya bayar da shawarar kan ƙaddamar da gangamin dashen itatuwa la’akari da mahimmancin kiyaye muhalli. Ya kuma jaddada buƙatar ƙara dasa itatuwa tare kuma da yaki a faɗin jihar.
A ƙarshe Sarkin na Bichi ya buƙaci gwamnati da masu hannu da shuni da dinga haƙar rijiyoyin burtsatse a faɗin jihar domin hakan ne zai samar da hanyoyin samar da ruwan sha mai tsafta da kuma rage wahalhalun da al’umma ke fama da su sakamakon ƙarancin ruwa da ake fuskanta.