Noman shinkafa zai haɓaka kuɗin shiga, tare da magance matsalar abinci a Kano – Korau

Must Try

Daga Abdulƙadir Haladu Kiyawa

Wani manomin shinkafa a jihar Kano, ya shirya wa wa gwamnatin jihar wani tsari mai kyau da zai haɓaka tattalin arzikin Jihar, yana mai ƙira ga gwamnatin da ta bawa bangaren noman shinkafa fifiko domin bunkasar kudaden shiga na cikin gida wato IGR.

Acewar manomin, za a iya cimma hakan ta hanyar amfani da dukiyar da Kano ke da ita ta filayen noma da kuma bullo da wasu ayyuka na musamman domin bunkasa darajar noma domin samun wadatuwar abinci.

Ya ce ‘’ noman shinkafa zai taimakawa jihar matuƙa wajen ci gaba da dogaro da kanta matukar za a yi amfani da damarmakin da ake da su na yin kasuwanci yadda ya kamata tare da tallafa wa manoma yadda ya kamata’’.

Da yake zantawa da Jaridar Farmers Voice a garin Kura, Shugaban kungiyar manoman shinkafa ta AGOLAS Malam Ado Kura ya ce ‘’Jihar Kano a matsayinta na cibiyar kasuwanci, tana da ƙarfin samar da kudaden shiga da zata iya biyan bukatun al’ummar jihar ba tare da dogaro da kason gwamnatin tarayya ba’’.

Ya kara da cewa, “Ya kamata gwamnatin Kano ta hada kai da cibiyoyin bincike tare da gano ayyuka na musamman da suka shafi noman shinkafa a lokacin rani da damuna”.

Korau ya kuma shawarci gwamnatin Jihar Kano da ta yi kokarin farfado da dukkanin madatsun ruwan da suka lalace da kuma kai shi zuwa yankunan da ake da filayen noma masu yawa tare da tabbatar da ingantaccen tsarin kula da albarkatun ruwa domin dorewar tsarin.

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img