Manoma a Maiduguri za su gudanar da ‘Sallar Roƙon Ruwa’

Must Try

Manoma a birnin Maiduguri na jihar Borno na shirye-shiryen gudanar da addu’o’i na musamman kan jinkirin saukar ruwan sama a jihar dake arewa maso gabashin Najeriya.

Al’amarin ya shafi manoma da galibinsu suka fito daga yankunan arewaci da tsakiyar jihar, inda suka ce suna son a hada kai ne domin neman taimakon Allah kan matsalar.

Ɗaya daga cikin manoman mai suna Ibrahim Ali ya koka da yadda suke ganin hadari kamar za a yi ruwan sama amma bayan wani lokaci sai ayi iska mai karfi hadarin ya washe.

Majalisar masarautar Borno, tace tana goyon bayan addu’o’in.

A wata sanarwa da ta fitar, Majalisar tace ta hada kan jama’a domin gudanar da addu’o’in rokon ruwan sama na musamman da aka shirya gudanarwa a yau Litinin 17 ga watan Yuli 2023 a dandalin Ramat da ke Maiduguri babban birnin jihar ta Borno.

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img