Majalisar Dinkin Duniya ta ware dala miliyan 20 domin a gaggauta daukar matakan dakile matsalar karancin abinci da abinci mai gina jiki a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Mataimakin kakakin MDD Farhan Haq ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a hedkwatar MDD dake birnin New York.
“Tare da dala miliyan tara daga Asusun Ba da Agajin Gaggawa da kuma dala miliyan 11 daga Asusun Ba da Agajin Gaggawa na Najeriya, za mu tallafa wa ƙoƙarin da gwamnati ke yi a jihohin Borno da Adamawa da kuma Yobe”
“Taimakon ya haɗa da samar da abincin ci nan take da samar da ruwan sha mai tsafta, da kula da lafiya da kuma bayar da tallafin noma,” in ji shi.