Ma’aikatar Gona ta gargadi jihohin Sokoto, Neja da Kwara kan ɓullar cutar Anthrax

Must Try

Daga Abdulkadir Haladu Kiyawa

Ma’aikatar Noma da Raya Karkara ta Najeriya na sake faɗakar da al’umma a karo na biyu game da barkewar cutar Anthrax a cikin makwabtan kasashe dake yammacin Afirka.

Cutar Anthrax dai cuta ce ta saeƙewar numfashi kuma ana samun ta ne a cikin ƙasa a mafi yawan lokuta tana shafar dabbobin gida da na daji, kuma mutane na iya kamuwa da cutar ta Anthrax idan sun yi hulɗa da dabbobi masu ɗauke da cutar.

Ta cikin sanarwar da ma’aikatar noma da raya karkarar ta fitar, ta bayyana alamun cutar ta Anthrax, wadanda suka hada da alamun mura da tari da zazzabi da ciwon jiki, Idan ba a gano cutar ba kuma an yi maganinta da wuri, tana iya haifar da ciwon huhu mai tsanani sannan tana wahalar numfashi ko kuma mutum ya rinka firgita idan ta yi tsanani kuma mutum zai iya mutuwa.

Sanarwar ta nanata cewa, duk shekara ana yin allurar rigakafin cutar Anthrax a Cibiyar Nazarin Dabbobi ta kasa da ke Vom a Jihar Filato, kuma wannan ita ce hanya mafi sauki na rigakafi da kuma magance cutar a jikin dabbobi.

Bisa la’akari da halin da ake ciki, ma’aikatar ta jaddada bukatar kara ƙaimi wajen gudanar da allurar rigakafin cutar ga dabbobi a jihohin Sokoto da Kebbi da Neja da Kwara da Oyo da Ogun da kuma Jihar Legas, sakamakon kusancin da suke da su da ƙasashen Burkina Faso da Togo da kuma Ghana.

Ma’aikatar noman da raya karkara ta kuma shawarci al’umma da su guji cin fatu (Ganda) da naman da ake yin bandar sa, da namun daji, domin suna da matukar haɗari.

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img