Janye Tallafi: Ana fargabar masu yin noman rani a jihar Yobe za su tafka asarar maƙudan kuɗaɗe

Must Try

Daga Abdulkadir Haladu Kiyawa

Tsadar Man fetur da ta takin zamani na barazanar ga ɗorewar noman ranin wasu manoma a jihar Yobe, lamarin da ya sanya suke kokawa ga Gwamnatin Tarayya da ta duba halin da suke ciki na fargabar tafka asarar maƙudan kuɗaɗen da su ka zuba a gonakin su.

Jaridar Farmers Voice NG ta tattauna da wasu manoman da suka nuna matukar damuwa bisa yadda al’amuran suka taɓarɓare sakamakon tsadar Man fetur din.

Guda cikin mahimman abubuwan da ake yi a noman rani shi ne ban ruwa, kuma ba zai yiwu ba sai da man fetur, domin a wadata amfanin gonakin da ruwan da suke buƙata.

Adamu Yusuf Barde, wani manomin shinkafa ne a ƙaramar hukumar Potiskum ta jihar Yoben ya ce kafin man fetur ya tashi matsalolin da suke fuskanta ba su da yawa, amma yanzu al’amuran duk sun ta’azzara, har ta kai ga amfanin su ya fara lalacewa sakamakon rashin samun kulawar da ta dace.

Ya ce “yanzu haka waɗanda su ke yi mana aiki a gonakin mu muke biyan su ba sa zuwa sakamakon sai sun hau Babur ko Mota ga shi kuma farashin sufuri ya yi tsada sakamakon tashin farashin man fetur”. Saboda haka muna kira ga gwamnatoci da su duba halin da muke ciki su kawo mana ɗauki”.

“Ni yanzu na zuba maƙudan kuɗaɗe a gonakin da nake noman shinkafa idan ban samu mafita ba zan tafka asarar sama da miliyan guda, kuma akwai ire-irena da su ma za su yi asarar da tafi haka wasu kuma bata kai haka ba”. Inji shi.

Yanzu haka dai ana sayar da Litar man fetur akan Naira 540, saɓanin Naira 190 da ake sayarwa a baya.

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img