Gwamnatin tarayya ta ƙara kuɗaɗen gudanar da cibiyoyin binciken aikin Gona – Farfesa Kabir Bala

Must Try

Aminu Halilu Tudun Wada

Shugaban jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria , Farfesa Kabir Bala, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta kara Samar da wadatattun kudaden gudanar da cibiyoyin binciken aikin Gona domin kara bunkasa Fannin Noma a Najeriya.

Farfesa Kabir Bala, ya bayyana hakan ne bayan kammala zagaya wasu daga cikin gonakin cibiyar jami’ar dake Samaru a Zaria, don ganin irin cigaban da ake samu a bangaren.

A yayin jawabin nasa , shugaban jami’ar ya ce cibiyar na cigaba da Samar da ingantaccen iri ga Manoma da zai taimaka musu Noma na Rani da Damina. Haka zalika shugaban ya bukaci gwamnatin tarayya da ta samar da karin kudaden bincike duba da halin da ake ciki na kara fadada bincike a zamanan ce a fadin Duniya.

“Akwai bukatar gwamnatin tarayya ta duba Fannin bincike don zuba kudade da kayan aiki na musamman wadatattu a bangaren Auduga da Gyada”

“Ana cigaba da fadada bincike a Duniya akan nau’ikan Noma da iri , don haka tilas ne mu fadada tare da yin aiki tukuru ta hanyar bincike don yin kafada da kasashen Duniya, amma abun takaici shi ne ana samun koma baya da hakan ba karamin illa zai yi ba wajen samar da wadataccen abinci a fadin kasar nan” inji Farfesa Kabir Bala.

A nasa jawabin shima ya yin zagayen babban shugaban cibiyar binciken aikin Gona na Jami’ar Farfesa Muhammad Faguji Ishaku, ya ce akwai bukatar al’umma su rungumi Noman Auduga da Gyada , kasancewar akwai alfanu sosai da ake samu a Fannin.

A cewar shugaban cibiyar matukar an Maida hankali wajen bangarorin Noman biyu, tabbas Arewacin Najeriya zai dawo da martabar sa tare da rage bukatar tallafi daga gwamnatin tarayya akan tattalin Arziki.

Muhammad Faguji Ishaku, ya ce Auduga da Gyada, a tarihi tun iyaye da kakanni daga yankin Arewa su suka gina kasar tare da samar da aiyyukan yi ,da habbaka tattalin Arziki don haka lokaci yayi da za a sake waiwaye wajen dawowa ka’in da na’in a bangaren.

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img