Fiye da Ƴan Najeriya Miliyan 2 ne za su iya faɗawa ƙangin yunwa a shekarar 2024

Must Try

Hukumar samar da abinci da bunkasa noma ta duniya ta ce ‘yan Najeriya akalla miliyan biyu da dubu 600, a jihohin Borno da Sokoto da Zamfara da kuma babban birnin kasar Abuja, na iya fuskantar matsalar rashin abinci a tsakanin watan Yuni da Agustan 2024.

Wakilin hukumar, Dr. Abubakar Suleiman ne, ya bayyana haka yayin gabatar da bayani na gargadin wurwuri ranar Juma’a a Abuja.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa bayanin, wani bangare ne na rahoto a kan tabbacin halin wadata al’umma da abinci, da kuma hasashe game da halin da za a shiga nan gaba.

A cewarsa, halin da ake ciki yanzu ya faru ne bayan wata damuna da ba a saba da ganin irin ta ba, wadda aka samu matsaloli da dama, wanda suka haɗa da ta’azzarar halin rashin tsaro kamar rikicin ƴan tayar-da-ƙayar-baya da na ƴan fashin daji.

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img