pornhub

Ɓeraye sun tilastawa manoma kwana a gonakinsu a Kano

Must Try

Wasu murguza-murguzan ɓeraye sun tilasta wa manoma kwana a gonakin su domin yin gadi, sakamakon ɓarna da su ke yi musu ta amfanin gona a yankin kananan hukumomin Kura, Bunkure da Garin Mallam a jihar Kano.

Manoman dai sun bayyana cewa ɓerayen sun zame musu annoba, musamman ma ganin cewa duk irin maganin kashe bera da aka saka musu, amma sai su ƙi ci, lamarin da ya sanya su ka ɗauki matakin yin fito-na-fito da su.

Sun kuma baiyana cewa idan suka durfafi gona to sai dai a yiwa manomi jaje, inda su ka ce ɓerayen ba sa tsoron mage ballantana muzuru.

Mallam Ahmed sani kura wani malamin gona ne ya yankin Dan Galawa dake karamar hukumar Kura daga kungiyar masu anfani da ruwan noman rani, ya yi kira ga gwamnati da ta kawo musu dauki.

Ya kuma yi kira ga masana da su bada gudunmawar hanyar da za a samu nasarar kashe ɓerayen ta hanyar zuba musu guba s abinci.

A nashi ɓangaren, Alhaji Sani Danladi Yadakwari, shugaban kungiyar masu noman tumatur ta kasa reshan jihar Kano ya ce wannan beraye sun dade suna uzzirawa manoma kuma suna zuwa ne lokacin sanyi.

Ya koka da cewa duk irin girman gonar manomi idan ba a yi wasa ba sai sun cinye ta.

“Wato wasu irin murguza-murguzan ɓeraye ne masu laifin basira domin duk irin maganin bera da ka saka musu a abinci banza su ci ba. Idan ka saka magani a abinci ka ajiye wani abincin maras magani, to maras maganin za su ci.

“Duk yawan shuka da aka yi sai sun cinye ta. Hakan ne ya sanya dole manoma da yawa su ka koma kwana a gonakin su domin gadin ganin gonar su da kuma kashe ɓerayen.

“Muna kira ga gwamnati da ta kawo mana dauki sannan muna kira ga masana ilimin dabbobi dansubtallafa mana da hanyoyi ko nau’in maganin da za a rika saka musu suna mutuwa,” in ji Yadakwari.

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img