Masu sana’ar sayar da ‘Ɗanyar Masara’ a Kano sun koka kan rashin matsuguni

Must Try

Masu sana’ar sayar da ɗanyar masara da ke garin Karfi a jihar Kano sun yi kira ga Gwamnan jihar Abba Kabiru Yusuf, da ya taimaka musu wajen samar musu da matsuguni na dindin a maimakon wanda aka ba su aro.

Kasuwar Ɗanyar masara ta Karfi da ke wajen birnin Kano a yankin karamar hukumar Kura, ta dade da kasancewa cibiyar kasuwancin ɗanyar masara a jihar.

Haka kuma ƴan kasuwar su na amfani da wani fili da ya kasance mallakin Dagacin Gundutse Alhaji Ibrahim Bassa da ke kan hanyar Kano zuwa Zaria fiye da shekaru ashirin. Kuma a halin yanzu Dagacin ya buƙaci filin na sa wanda hakan ya jefa ƴan kasuwar cikin fargaba.

Malam Hamisu Abdullahi wanda ya yi magana a madadin ‘yan kasuwar ya bayyana damuwarsa ga Jaridar Farmers Voice.NG, tare kuma da jaddada bukatar a sake tsugunar da ‘yan kasuwar cikin gaggawa, duba da yadda kasuwar ke karuwa da kuma karuwar hada – hada daga fadin jihohin ƙasar nan.

Malam Hamisu Abdullahi ya ƙara da cewa a baya sun tuntubi shugaban karamar hukumar Kura, Mustapha Bala, inda suka bumaci a samar musu da fili mai fadin hekta 3 mallakin gwamnati.

“Filayen da mu ka bayar da shawarar da a yi amfani da shi wajen tsugunar da mu a matsayin kasuwar Danyar Masara ta dindin ya na kusa da cibiyar wasanni ta jihar Kano, da ke garin Karfi, kuma ba shi nisa da kasuwar mu,”

Ya kuma bayyana cewa a karon farko da suka gabatar da shawarar ga shugaban ƙaramar hukumar ya tabbatar musu kan cewa zai duba bukatar ta su.

Duk da ƙarancin fili a Kasuwar Masara ta Karfi, tana samun nasarar sayar da danyar masara a duk shekara wanda kudinta ya kai Naira miliyan 200, kamar yadda wasu bayanan da jaridar FARMERS VOICE NG ta su.

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img