Ƴan bindiga sun hallaka manoma tare da sace wasu da dama a jihar Kaduna

Must Try

‘Yan bindiga sun kashe mutum uku tare da sace wasu da dama a wani hari da suka kai garin Sabo Layi da ke yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Shugaban ƙungiyar ci gaban masarautar Birnin Gwari (BEPU) Usman Kasai, wanda ya tabbatar da kai harin, ya ce yanzu haka suna ƙoƙarin tantance yawan adadin mutanen da aka yi garkuwa da su zuwa cikin daji.

Rahotonni sun ce ‘yan bindigar sun far wa ƙauyen ranar Alhamis, inda suka riƙa harbin kan-mai-uwa-da-wabi, lamarin da ya haddasa mutuwar mutum uku.

Jihar Kaduna wadda ke arewacin Najeriya na ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga, waɗanda ke garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

Yawaitar garkuwa da mutane da hare-haren ‘yan fashin daji a yankin arewa maso yammacin Najeriya na ɗaya daga cikin ƙalubalen tsaro da ya daɗe yana ci wa ƙasar tuwa a ƙwarya.

Baya ga rikicin Boko Haram da ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum 40,000 a yankin arewa maso gabashin ƙasar, tun shekarar 2019.

Ga kuma ayyukan ‘yan bindiga a yankin kudu maso gabashin ƙasar, waɗanda ke kai wa jami’an tsaro hare-hare.

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img