Ƙungiyar manoma ta AFAN ta buƙaci mambobinta da su yi hattara da ƴan damfara

Must Try

Abdulƙadir Haladu Kiyawa

Kungiyar manoman Najeriya AFAN ta yi gargadi ga manoman ƙasar da su ƙauracewa duk wani saƙo da ke nuna cewar za a biya wani kuɗi domin yin rijistar zama mamba a ƙungiyar.

Ƙungiyar ta kuma shawarce su da su guji biyan kuɗi ga wasu mutane da ke da’awar fito da sassauƙar hanyar zama mambobi a ƙungiyar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, shugaban ƙungiyar ta AFAN na ƙasa Architect Kabir Ibrahim, ya bayyana damuwarsa kan illar da irin waɗannan ayyukan ɓatagarin ke yi ga manoman Najeriya.

Bisa la’akari da ɗumbin ƙalubalen da manoman su ke fuskanta, ya yi Allah-wadai da matakin neman a biya kuɗin yin rijistar zama mamba a ƙungiyar a wannan lokaci mai tsanani.

A cewar Kabir Ibrahim, waɗannan ɓatagarin mutane tuni sun turawa mutane wani adreshi, inda suka umarce su da su biya kuɗi domin a sake sabunta musu rijistar zama mambobi a ƙungiyar ta kasa.

Ya kuma jaddada cewa wannan buƙata yaudara ce kuma ƙungiyar ta AFAN ba ta da masaniya akai.

A ƙashe shugaban AFAN ɗin na ƙasa ya yi ƙira ga manoma a duk faɗin kasar da su yi watsi da makamantan waɗannan saƙonnin na bogi.

- Advertisement -spot_img

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest Recipes

- Advertisement -spot_img

More Recipes Like This

- Advertisement -spot_img