Gwamnatin kasar Norway ta bayar da ƙarin Dala miliyan 4.5 domin tallafawa ayyukan agaji na hukumar kula da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya FAO, domin magance matsalar da ta kunno kai a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Wakilin hukumar kula da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya FAO a Najeriya da kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, Fred Kafeero, ne ya bayyana haka a lokacin rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin hukumar ta MDD da gwamnatin Norway a birnin tarayya Abuja.
Kafeero ya ce tallafin da gwamnatin ƙasar Norway ta bayar ya kai dalar Amurka miliyan 24, tun farkon rikicin Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya, kuma sama da mutane miliyan ɗaya waɗanda rikici ya shafa sun amfana da tallafin.
A cewarsa, tun daga shekarar 2017, gwamnatin ƙasar Norway, ta hannun ma’aikatar harkokin wajen kasar, ta ba da gudummawa sosai wajen sake gina rayuwar al’ummomin da suka fi fama da rauni a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, wadanda sama da shekaru goma ke fama da rikicin Boko Haram.
Tallafin kuɗin dai za a yi amfani da shi wajen aiwatar da ɗorewar ayyukan da ake yi domin inganta samar da abinci mai gina jiki tare samar da rayuwa mai inganci a jihohin Borno da Adamawa da Yobe da kuma jihar Taraba.